Namadi Sambo na ziyara a Borno

Najeriya
Image caption Jahar na daga cikin jahohin da ake kai yawan hare hare

A ranar Lahadi ne mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Namadi Sambo ya kai wata ziyarar gani da ido a jahar Borno da ke arewacin kasar.

Wannan dai ita ce ziyara ta farko da mataimakin shugaban kasar ya kai a wannan jaha tun bayan barkewar rikici a cikin jahar.

A lokacin wannan ziyara zai tattauna da hukumunin jahar kan maganar tsaro da zaman lafiya a wannan jaha.

Ziyarar ta wakana ne a dai lokacin da da al'ummar jahar ke son ganin zaman lafiya mai dorewa ya tabbata a cikifadin jahar baki daya.

Kwomishinan watsa labarai a jahar ta Borno na cewa Inuw Bwala ya fadawa BBC cewa batun tsaro na daga cikin irin abubuwan da mataimakin Shugaban Kasar zai tattauna da hukumomin jahar.

Karin bayani