Rasha na son ganawa da 'yan adawar Syria

Sergei Lavrov
Image caption Sergei Lavrov ya jaddada adawar Rasha da tsoma ta fuskar soji a Rikicin Syria

Rasha ta ce ta na so ta rika tuntubar ’yan adawar Syria akai-akai, bayan wata tattaunawa ta farko a tsakanin bangarorin biyu—Rasha da ’yan adawar.

A lokacin tattaunawar, wadda aka yi yayin wani taron kasa-da-kasa a kan tsaro a birnin Munich na kasar Jamus, Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya gayyaci shugaban kawancen ’yan adawar Syria, Ahmed Moaz al-Khatib Moscow.

Tun da fari, yayin wani taron manema labarai, Mista Lavrov ya jaddada kin amincewa da kiran da ake yi na Majalisar Dinkin Duniya ta tsoma baki a rikicin na Syria.

A cewarsa, “Duk wata barazana ta amfani da karfin soji ba za ta samu karbuwa ba, ba kawai doan muna tuna abin da aka yi da kudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a Libya ba, sai don a halin da ake ciki muna ganin ba a bukatar karin makamai a Syria”.

Karin bayani