Sasantawa tsakanin gwamnati da kabilar Burma

Image caption Shugaban Burma, Thein Sein

A ranar Litinin ne ake sa ran fara tattaunawa tsakanin jami'an gwamnatin Burma da 'yan tawayen kabilar Kachin da ke arewacin kasar a wani gari da ke kan iyakar kasar China.

Dakarun 'yan tawayen Kachin sun bukaci kasar China - wacce ke nuna damuwa game da karuwar rikicin da ke faruwa - ta jagoranci tattaunawar.

Dubban fararen hula ne suka rasa muhallansu a fadan da ake yi tsakanin 'yan tawayen da dakarun gwamnati bayan da dakarun gwamnati suka yi amfani da jiragen yaki da manyan makamai a kokarin su na tarwatsa 'yan tawayen.

Rahotanni sun ce bangarorin biyu sun kasa cimma matsaya kan ko a rattaba hannu a kan wata yarjejeniya gabanin ko kuma bayan an zayyana wani shiri na siyasa.

Karin bayani