Cameron na ganawa da Karzai, Zardari

Image caption Karzai, da Cameron da Zardari

A ranar Litinin ne Firayim Ministan Burtaniya, David Cameroon, zai gana da shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai da takwaransa na kasar Pakistan Asif Ali Zardari a gidansa da ke wajen birnin London.

Shugabannin uku za su tattauna ne a kan hanyoyin da za a bi don tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasashen Pakistan da Afghanistan don hana mayaka 'yan kungiyar Taliban farfadowa da zarar dakarun kasashen duniya sun kammala aikace-aikacen su a Afghanistan a badi.

An saki wadansu shugabannin Taliban daga gidajen yarin Pakistan, sai dai Afghanistan na so ne a saki wadansu da dama, cikinsu har da tsohon kwamandan kungiyar, Mullah Baradur.

Pakistan dai na so ne a kawo karshen harin da ake kai wa a kasar da jiragen saman Amurka marasa matuki, kana a bayar da tabbacin tsaron lafiyar 'yan kasar.

A yayin da wa'adin da kungiyar tsaro ta NATO ta dibarwa kan ta na mika jagorancin tsaron Afghanistan ga hukumomin kasar a shekarar 2014 ke matsowa, Shugaba Karzai ya shaidawa BBC cewa ba ya so a yi kuskure irin wanda ya faru lokacin da Russia ta janye daga kasar kusan shekaru 25 da suka gabata, lamarin da ya yi sanadiyar jefa ta cikin yakin basasa.

Karin bayani