Ranar yaki da cutar sankara

Image caption Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon

Litinin ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don tunawa da mutanen da ke fama da ciwon sankara ko Cancer, ana wayar da kan jama'a game da cutar mai saurin halaka bil adama.

Likitoci sun ce shan taba, da giya da kuma cin abincin gwangwani na cikin abubuwan da ke yin sanadiyar kamuwa da cutar.

Alkaluma sun nuna cewa kimanin kashi 45 cikin 100 na masu fama da cutar suna zaune ne a kasashe masu tasowa.

Jami'an lafiya sun ce adadin masu kamuwa da cutar yana karuwa.

Masu fama da cutar suna kokawa game da rashin samun magungunan cutar cikin sauki.

Masana kiwon lafiya sun yi kira da a kauracewa dabi'un da ke haddasa cutar.

Karin bayani