Faransa na gadin mahakar ma'adinan Nijar

Image caption Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta ce sojojin kasar Faransa na musamman suna gadin mahakar ma'adinin uranium ta kasar.

Shugaba Mahamadou Issoufou ya shaidawa wata kafar watsa labarai ta kasar Faransa cewa sun dauki matakin ne da nufin inganta tsaro a wuraren hakar ma'adinai sakamakon garkuwar da aka yi da wadansu mutane 'yan kasashen waje a wani wajen hakar iskar gas da ke kasar Algeria kwanakin baya.

Kamfanin Faransa mai suna, Areva, shi ne babban kamfanin da ke hakar ma'adinin uranium a Nijar- wacce ita ce kasa ta biyar da ta fi yawan uranium a duniya.

A shekaru uku da suka gabata wadansu masu kaifin kishin Islama sun sace 'yan kasar Faransa guda hudu wadanda ke aiki da kamfanin Areva a Nijar.

Karin bayani