Iraq: An hallaka mutane 16 a Kirkuk

Image caption Wurin da aka kai hari a Kirkuk

Jami'ai a garin Kirkuk dake arewacin Iraqi sun ce an kashe mutane goma sha shida a wani harin ƙunar baƙin wake da aka ƙaddamar a hedikwatar 'yan sanda.

Wani wakilin BBC a birnin Baghdad yace bayan fashewar wani abu, wasu 'yan ƙunar baƙin wake su biyu sanye da kayan sarki, ɗauke da manyan bindigogi suka farma hedikwatar 'yan sandan

Sai dai ɗan sanda ya harbe daya daga cikinsu, gudan kuma aka raunata shi a lokacin da yake ƙoƙarin tada bom din dake jikinsa.

Iraqi dai ta jima tana fama da tashin hankali tun daga bayan kifar da gwamnatin Saddam Husseini da Amurka ta jagoranta.