Shugaba Asad na Syria ya gargadi Isra'ila

Shugaba Asad na Syria
Image caption Syria tace zata tunkari duk harin da aka kai mata daga Israila

A kalaman da yai na farko tun lokacin da Isra'ila ta kaddamar da hare haren sama a cikin Syria, Shugaba Bashar Al Asad yace kasar sa nada karfin tunkarar duk wani hari da za 'a iya kai mata

Ya kuma zargi Israilan da hade kai da wasu mutane dake ciki da kuma wajen Syria, wadanda suke neman ganin tabarbarewar rikici a cikin Kasar

A kalaman da tai na farko, itama Israela tace hare haren na nuna cewa ba zata bari a kai manyan makamai cikin makwabciyar kasar ba

Jami'an Amurka dai sunce an kaddamar da hare haren saman ne akan makamai masu linzamin da ake kokarin kaiwa 'yan kungiyar Hizbullah, wacce take a Labanon

Karin bayani