An yi luguden wuta kan sansanonin 'yan tawayen Mali

Jirgin yaki a Mali
Image caption An kai hari kan sansanonin 'yan tawaye a kusa da Kidal

Rahotanni daga arewacin Mali na cewa jiragen yakin Faransa sun yi barin wuta akan sansanonin masu kaifin kishin Islama dake kusa da garin Kidal

Dakarun Faransan dana Malin na kokarin tsare garin ne, wanda shine gari na karshe da 'yan tawayen suke da karfi, biyo bayan kwace garuruwan Timbukutu da kuma Gao

A ranar laraba sojojin Faransan sun kwace ikon filin jirgin garin na Kidal

Wannan barin- wuta dai, ya biyo bayan ziyarar da shugaban Faransan Franswa Hollande ya kai zuwa Malin a ranar asabar

A lokacin ziyarar Shugaban Faransan yace dakarunsa zasu zauna a Kasar har sai an jibge dakarun Afirkan da zasu kare kasar

Karin bayani