Kotu ta daure wani mai fafutuka a Kuwait saboda zagin Sarki

Sarkin Kuwait
Image caption Ana daure masu fafutuka a Kuwait

Wata kotu a Kuwait ta yanke- wa wani mai fafutuka kuma dan adawa, Mohammed Eid al- Ajimi hukuncin daurin shekaru biyar, saboda samunsa da laifin zagin Sarkin Kuwaitin a shafin Twitter

Karkashin kundin tsarin mulkin Kuwait, an bayyana Sarkin a matsayin mutumin da baya tabuwa

Wani mai magana da yawun Al'ummar Kuwaiti ta kare hakkin Dan adam, Mohammed al Humaidi yace an yankewa wasu matasa biyu suma masu fafutukar hukuncin daurin shekaru biyu -biyu, saboda aikata irin wannan laifi a watan daya gabata

Karin bayani