Najeriya: 'Za'a baiwa masu bankaɗo zamba kariya'

Image caption Goodluck Jonathan, shugaban Najeriya

A Najeriya, wani kwamitin shari'a na majalisar wakilan kasar ya gudanar da sauraron ra'ayoyin jama'a a kan wani ƙudirin dokar da za ta ba da kariya ga masu bankaɗar masu aikata miyagun laifuka a ƙasar.

Ƙundirin dokar dai ya yi tanadin wani abin tukwici ga waƊanda suka ba da bayanai da suka taimaka wajen cafke masu laifi.

Cikin 'yan shekarun nan dai ana samu karuwar zarge-zargen cin hanci da rashawa a kusan dukkan ɓangarorin gwamnati.

Najeriya dai na daga cikin ƙasashen dake da arziƙi, amma jama'arta ke fama da talauci.