Malala ta sadaukar da ranta ga taimako

Malala Yusufzai
Image caption Malala Yusufzai

Yarinyar nan 'yan kasar Pakistan wacce 'yan Taliban suka harba a ka, sakamakon fafutukar da take yi na ganin an samar da ilimi ga 'yan mata, ta ce ashirye take ta sadaukar da ranta kan wannan manufa.

Malala Yousufzai, wacce ke da shekeru 15 da haihuwa, tana karbar magani ne a wani asibiti a birnin Birmingham na nan Ingila, tun watan Oktoban da ya gabata.

A wani sakon bidiyo da ta yi kafin tiyatar da aka yi mata ta baya-bayan nan, ta ce tana samun sauki, kuma Allah ya taimaka mata, a don haka itama tana so ta taimaki mutane.

Ana ta kiraye-kirayen a sanya sunan Malala a jerin wadanda za a iya baiwa kyautar zaman lafiya ta Nobel.