'Gwamnatin Najeriya ba ta hukunta 'yan sanda'

Image caption Tambarin Amnesty International

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta yi zargin cewa gwmnatin Najeriya ba ta gudanar da cikakken bincike da hukunta 'yan sandan kasar da ake zargi da laifin kisan gilla.

A wani rahoto da ta fitar ranar Talata, kungiyar ta Amnesty ta ce a lokuta da dama iyalan wadanda aka kashe kan shiga cikin mawuyacin hali sakamakon rashin samun cikakkun bayanai daga hukumomin shari'a a Najeriya game da makomar 'yan uwansu da aka kashe.

Amnesty, wacce ta gudanar da bincikenta a jihar Rivers da ke yankin Niger Delta, ta yi amannar cewa haka batun yake a sassa daban-daban na kasar.

Ta zargi wadansu likitoci da hada baki da 'yan sanda ta yadda ba sa gudunar da cikakken bincike a kan gawarwarkin mutanen da ake kai wa asibitoci bayan an halaka su.

Karin bayani