'Yan majalisar Burtaniya sun amince da auren jinsi guda

'Yan majalisar dokoki a Burtaniya
Image caption Auren jinsi guda ya janyo cece kuce a Burtaniya

Mambobin majalisar dokokin Burtaniya sun kada kuri'ar amincewa da kudurin da ake ta cece-kuce, wanda zai bayar da damar auren jinsi guda a kasashen Ingila da Wales.

Kudurin wanda aka amince da shi da gagarumin rinjaye na kuri'u dari hudu da kuma dari da saba'in da biyar.

Hakan ya nuna cewa kusan rabin 'ya'yan jam'iyyar Conservative mai mulkin kasar sun kada kuri'ar kin amincewa ko kuma sun kaurace wa kuri'ar.

Kudurin ya samu goyon bayan karamar jam'iyyar hadaka ta Liberal Democrats da kuma ta 'yan adawa wato Labour.

Tuni dama dai aka amince da zaman 'yan madugo ko luwadi wuri guda a kasar.

Karin bayani