Bulgaria ta zargi Hezbollah da hannu a wani hari

Hassan Nasrallah, shugaban Hezbollah
Image caption Bulgaria na zargin Hezbollah da kai hari

Kasar Bulgariya ta ce akwai hannun kungiyar kaifin kishin Islama ta Hizbullah a wani harin bam da aka kai a kusa da gabar ruwan tekun Bahar Aswad cikin watan Yulin bara, inda aka kashe wasu 'yan kasar Isra'ila biyar da kjuma direban moitar su dan kasar Bulgaria.

Jami'ai a Sofia, babban birnin kasar, sun ce bincike ya nuna cewa biyu daga cikin mutane uku da ake zargin suna da hannu a harin bam din 'yan kungiyar Hizbullah ne

Ministan cikin gida na kasar Bulgariar Tsvetan Tsvetanov yace an tabbatar hakika cewa mutane ukku ne su ka kai harin, kuma daya daga cikin su ya rasa ransa a cikin motar da Bus din, yayin da ragowar biyun kuma su ka tsere.

Yace ''jami'an Bulgaria masu gudanar da bincike sun hakikance mutanen biyu 'yan kasashen Canada ne da Australia kuma mambobi ne na kungiyar Hizbullah."

Ministan ya baiyana wannan ne bayan taro na tsawon sao'i shidda da yayi da majalisar kwaron kasa inda a lokacin ne kuma aka sanar da shugabannin kasar game da sakamakon bincikewn da aka gano.

Shi ma da yake tsokaci Rob Wainwright Daraktan yan sandan tarayyar Turai Europol wadda ke taimakawa wajen tsara manufofin ayyukan yan sanda a kasashen kungiyar tarayyar Turai yace dukkan alamu sun nuna akwai sa hannun Hizbullah a harin.