Kidal ya fada hannun dakarun Faransa

Sojojin Faransa a Mali
Image caption Sojojin Faransa a Mali

Rundunar sojin Faransa ta ce dakarunta da na kasar Chadi sun shiga cikin garin Kidal na arewacin Mali, wanda shi ne na baya-bayan nan da ya fadi daga hannun 'yan tawaye wadanda suka kwace iko da arewacin kasar watanni goma da suka gabata.

Mai magana da yawun sojin Faransa ya ce kusan dakarun Chadi 1,800 ne suka shiga cikin garin, yayin da na Faransa suka kwace filin saukar jiragen saman birnin.

Wani mazaunin garin na Kidal yace al'amura sun kazanta.

A baya za ka iya yawo a Kidal har karfe 3 na dare, amma tun da dakarun Faransa suka shigo, mutane ke taka-tsan-tsan, saboda sojojin na neman mutane su nuna katin shaida.

A wani labarin kuma yanzu haka shugabannin kasashen duniya na gudanar da taro kan kasar ta Mali a birnin Brussels na kasar Belgium.

Wakilan MDD da Tarayyar Turai da ta Afrika, na duba yiwuwar yadda za a shirya zabe a kasar nan gaba a bana, da kuma ayyukan jin kai.

Karin bayani