Jam'iyyun adawar Najeriya sun hade

Janar Muhammadu Buhari da Cif Bola Ahmed Tinubu
Image caption Manyan jagororin 'yan adawa a Najeriya, Janar Muhammadu Buhari da Cif Bola Ahmed Tinubu

Manyan jam'iyyun adawar Najeriya da suka hadar da ACN da APGA da ANPP da CPC sun bayar da sanarwar hadewa karkashin sabuwar jam'iyyar All Progressive Congress domin kalubalantar jam'iyyar PDP mai mulki a zabe mai zuwa.

Sanarwar hakan na dauke da sa hannun shugabannin kwamitocin da jam'iyyun suka kafa domin tattaunawa kan batun hadewar tasu.

Shugabannin su ne Cif Tom Ikimi na jam'iyyar ACN da Mallam Ibrahim Shekarau na jam'iyyar ANPP da Alhaji Garba Gadi na jam'iyyar CPC da kuma Annie Okonkwo, APGA.

Jam'iyyun sun ce sun amince ne su kafa sabuwar jam'iyya da za ta mutunta siyasar cikin gida, da kuma mayar da hankali kan abubuwan da ke ci wa 'yan Najeriya tuwo a kwarya, wadanda suka hadar da kawar da cin hanci da rashawa, da samar da tsaro da kuma bunkasa tattalin arziki.

A jiya ne dai gwamnonin jihohi goma da suka fito daga jam'iyyun adawar daban-daban suka ce sun amince su dunkule waje guda don samar da jam'iyyar da za ta kalubalanci jam'iyyar PDP mai mulki a zabukan da ke tafe.

Gwamnonin sun bayyana yunkurin nasu da cewa yana da matukar muhimmanci saboda ceto kasar daga matsalolin da take ciki, wadanda in ji su jami'iyar PDP ta kasa magancewa.

A shekarar 2011 dai, jam'iyun ACN da CPC sun yi kokarin tsayar da dan takarar da zai fuskanci jam'iyyar PDP amma lamarin ya ci tura.

Jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriyar dai ta ce a shirye take ta fafata da duk wani shiri da jam'iyyun adawar suka yi.

Karin bayani