Gibin tattalin arziki a tsakanin 'yan China

Tattalin arzikin China na bunkasa
Image caption Tattalin arzikin China na bunkasa

Gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin magance wagegen gibin da ake cigaba da samu tsakanin masu hannu da shuni da kuma talakawa a kasar.

Majalisar kolin China ta fitar da wasu ka'idoji, kuma tace garambawul ya zama dole domin rarraba kudaden shiga cikin adalci.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin China masu ra'ayin kwaminisanci ke nuna damuwa game da rashin daidaito da ka iya yin barazana ga siyasar kasar.

A yayin da China ta bunkasa zuwa kasa ta biyu mafi girman tattalin arziki a duniya, wasu 'yan kasar sun zama hamshakan masu kudi, yayinda kuma ake samun masu rufin asiri.

Sai dai kuma gibin dake tsakanin masu kudi da talakawa na zama wagege.

A kasar da jam'iyyar kwamunis ke jagoranta, rashin daidaito na neman jefa siyasar kasar cikin tangal-tangal.

Saboda haka ne shugabannin kwamunisancin suka bullo da wasu sababbin ka'idoji na yin garmbawul.

Hikimar dai ita ce ta tsamo mutane miliyan 80 daga kangin talauci nan da shekaru uku.

Haka kuma a rubanya kudaden shigar kowa sau biyu nan da shekarar 2020, ta hanyar bunkasa kudaden shigar talakawa manoma da kuma rubanya albashi mafi karanci a birane.

Masu sharhi

Manyan masana'antu mallakin kasar za su mika ribar da suke samu domin sanyawa a harkar kiwon lafiya da ilimi da kuma gidaje masu rahusa.

Sai dai wasu masu sa ido kan al'amura na nuna shakku, domin an dauki shekaru biyu ana aiki a kan ka'idojin, kafin a fito da su.

Ka'idojin kuma sun kunshi buri da dama, amma manufofi kalilan.

Masu karfin fada a ji da wadanda ake zargin suna da wasu bukatu na son zuciya a tsarin tafi da al'amuran kasar sun taimaka wajen samun jinkirin fito da ka'idojin.

Haka kuma akwai yiwuwar su yi kafar ungulu ga yunkurin garambawul din.

Akwai mutane da dama dake adawa da mallakar sababbin gidaje da haraji kan gado ko garambawul game da fannin kudin kasar.

Sannan wasu na adawa da tsarin nan na izinin zama a guri, abin da ke hana mutane da dama yin hijira zuwa manyan biranen kasar.

Su kansu ka'idojin sun bayyana cewa mayar da kasar China wajen da ake adalci, abu ne mai wuya da kuma sarkakiya, kuma ba abu bane da za a cimma farat daya ba.