Mata sun koka da matsalar fyade a Afirka ta Kudu

Fyade a Afirka ta Kudu
Image caption Ana samun karuwar aikata fyade a Afirka ta Kudu

Kungiyoyin mata na jam'iyyar ANC mai mulkin Afrika ta Kudu, sun koka kan yadda ake samun karuwar aikata fyade a kasar, bayan da wata yarinya ta mutu sakamakon fyaden da wasu gungun mutane su ka yi mata a yammacin birnin Cape Town. Kungiyar matan sun ce lamarin ya kada su.

Yarinyar 'yar shekaru sha bakwai da haihuwa - an ce ta bayyana daya daga cikin wadanda su ka kai mata harin kafin ta mutu, kuma yanzu haka 'yan sanda na tsare da wani mutum guda.

Afrika ta Kudu na daya daga cikin kasashen da aka fi aikata laifukan fyade a duniya.

Wakilin BBC ya ce ba kamar kasar India ba, inda a kwanakin nan ake ta nuna damuwa kan batun fyade, batun ba haka yake ba a Afrika ta Kudu, inda ba a jin duriyar yawancin fyaden da ake aikata wa.

Karin bayani