An gwabza kazamin fada a kewayen Damascus

Syria
Image caption An tafka kazamin fadan da aka jima ba a ga irin sa ba.

Rahotanni daga kasar Syria na cewa ana gwabza kazamin fada da aka shafe watanni ba a yi irinsa ba a kewayen birnin Damascus.

Mazauna yankin sun ce sun yini suna jin karar bama-bamai, yayin da jami'an tsaro su ka ce sojoji na kaddamar da hare-hare.

Yankunan birnin Damascus da dama sun koma sansanin 'yan tawaye a 'yan watannin da suka wuce.

A taron da ake yi na kungiyar kasashen Musulmi a birnin Alkahira na Masar, shugaban babbar kungiyar adawa ta Syria, ya ce wajibi ne gwamnatin kasar ta fara sakar mutanen da ta ke tsare da su nan da ranar Lahadi, idan har tana son shiga kiran tattaunawar da ya yi.

Karin bayani