An kashe Shokri Belaid na Tunisia

Shokri Belaid
Image caption Shokri Belaid, mai adawa da gwamnatin Tunisia

An harbe har lahira wani fitaccen mai adawa da gwamnatin masu matsakaicin ra'ayin musulunci ta Tunisia.

'Yan uwa da abokan Shokri Belaid, na jam'iyyar Unified Democratic Patriot Party, an harbe shi ne aka da kuma cinya a wajen gidansa da ke birnin Tunis.

Shugaban kasar Tunisia Moncef Marzouki, wanda yau ya katse ziyarar da yake yi a Faransa da kuma taron kasashen Musulmai da aka shirya yi a Masar, ya ce ba za a amince da harin ba.

Inda ya ce wannan barazana ce kuma tamkar wani wani sako ne aka turo da ba za su karba ba. Kuma ya lashi takobin ci gaba da yaki domin kawar da makiya juyin-juya hali.

Dubban jama'a sun fita kan tituna a biranen Tunis da Sidi Bouzid -- inda yujin-juya halin kasar ya fara - domin yin Allah wadai da kisan.