Wasu jam'iyyun adawa a Tunisia sun kira yajin aikin gama gari

Shokri Belaid
Image caption Shokri Belaid, mai adawa da gwamnatin Tunisia

Gamayyar jam'iyyun adawa ta 'yan ba ruwanmu da addini a Tunisia, sun ce za ta fice daga kwamitin rubuta kundin tsarin mulkin kasar, sannan su ka yi kira ga magoya bayan su da su shiga yajin aikin gama-gari, bayan da aka yi wa daya daga cikin shugabanninsu kisan gilla

An harbe har lahira Shokri Belaid wani fitaccen mai adawa da gwamnatin masu matsakaicin ra'ayin musulunci ta Tunisia.

Shugaban kasar Tunisia Moncef Marzouki, wanda yau ya katse ziyarar da yake yi a Faransa da kuma taron kasashen Musulmai da aka shirya yi a Masar, ya ce ba za a amince da harin ba.

Inda ya ce wannan barazana ce kuma tamkar wani wani sako ne aka turo da ba za su karba ba. Kuma ya lashi takobin ci gaba da yaki domin kawar da makiya juyin-juya hali.

Dubban jama'a sun fita kan tituna a biranen Tunis da Sidi Bouzid -- inda yujin-juya halin kasar ya fara - domin yin Allah wadai da kisan.