Sabbin shaidu kan yaron da matsafa suka kashe a London

Wani yaro da ya taba fadawa hannun matsafa a Uganda
Image caption Wani yaro da ya taba fadawa hannun matsafa a Uganda

Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano sabbin shaidu game da kisan da aka yi ma wani yaro dan Afrika, wanda aka tsinci gangar jikinsa a kogin Thames dake London, shekaru sha biyu da suka wuce.

An kashe shi ne domin yin tsafi da wasu sassan jikinsa, kuma kasancewar jami'an tsaron dake gudanar da bincike ba su gane ko wanene ba ne, sai suka rada masa suna Adam.

Yanzu a karon farko, wata muhimmiyar mai bayar da shaida, wata mata mai suna Joyce ta fada wa BBC cikakken sunan yaron, tana mai cewa sunansa Patrick Erhabor, kuma dan asalin garin Benin ne a jihar Edo, dake kudancin Nijeriya.

Matar ta kuma bayyana sunan mutumin da ta ce shi yayi safarar yaron zuwa Ingila.