Amurka ta tsaurara takunkumi a kan Iran

Image caption Shugaban Iran Mahmoud Ahmedinijad

Gwamnatin Amurka tana fadada takunkumin da aka kakabawa kasar Iran da nufin tursasawa gwamnatin kasar yin watsi da shirinta na nukiliya.

A yanzu dai Amurka na tilastawa a ajiye kudaden da Iran ta samu daga cinikin danyen man ta a kasashen da suka hada da China da, India da kuma Turkiya, a wani asusu na kasashen maimakon kwaso kudaden zuwa kasar Iran.

Kazalika, cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen duniya da ke huldar kasuwanci da Iran na fuskantar barazanar cire su daga tsarin harkokin kasuwanci a Amurka, matukar suka karya wannan sabon sharadi da aka gindaya mu su.

Karin bayani