'Palasdinawa na tattaunawa a kan gwamnatin hadin kai'

Image caption Khaled Meshaal

Jagoran kungiyar Hamas ta Palasdinawa, Khaled Meshaal, ya shaidawa BBC cewa yana tattaunawa da shugaban Palasdinawa, Mahmoud Abbas, kan yiwuwar kafa gwamnati hadin kai tsakanin kungiyar Hamas da kuma jam'iyar Fatah ta shugaban kasar.

Ana ci gaba da samun kyautatuwar dangantaka tsakanin kungiyoyin biyu a 'yan watannin nan.

Khaled Meshaal ya ce: '' Za mu ci gaba da sasantawa. Ko a jiya ma na kira dan uwa na Abu-Mazin (Abbas) ta wayar tarho; a ranar Juma'ar da ta gabata mun gana da shugabannin riko na kungiyar samun 'yancin kan Palasdinawa a birnin Alkhira na Masar inda muke duba yiwuwar kafa gwamnatin hadin kai''.

Rashin jituwar da ke tsakanin bangarorin biyu ya sanya ba a yi zaben shugaban kasa dana 'yan majalisar dokoki a shekaru da dama ba.

Karin bayani