Amurka na taimakawa 'yan tawayen Syria

Leon Panetta
Image caption Leon Panetta, sakataren tsaron Amurka mai barin gado

Satakaren tsaron Amurka mai barin gado, Leon Panetta, ya ce ya goyi baya, kuma har yanzu yana goyon bayan taimakawa 'yan tawayen Syria da makamai.

Kalaman na Mr Panetta su ne na farko da wani babban jami'i na Amurka ya furta.

Ya ce ya goyi bayan shirin da tsohuwar sakatariyar harkokin waje Hillar Clinton da daraktan hukumar leken asiri ta CIA David Petraeus, suka gabatar na baiwa 'yan tawayen na Syria horo da kuma makamai kai tsaye.

Sai dai fadar White House ta yi watsi da shirin, saboda Obama ba ya son sanya hannu a rikicin a lokacin da yake fuskantar zabe.

Wakiliyar BBC ta ce gwamnatin Amurka na dari-darin taimakawa 'yan tawayen kai tsaye.

Sai dai kawayenta kamar Qatar da Turkiyya, suna baiwa 'yan twayen makamai da masaniyar Amurkan.

Karin bayani