Rikicin siyasar Tunisia na kara kamari

Masu zanga-zanga a Tunisia
Image caption kungiyoyin 'yan adawa hudu na kasar sun sanar da janye wa daga majalisar dokokin kasar, biyo bayan kisan

Rikicin siyasar Tunisia na kara kamari, bayan kisan gillar da aka yi wa shugaban 'yan adawa a farkon makon nan.

Kisan mai adawa da Musuluncin, Chokri Belaid ya janyo zanga-zanga, inda firai ministan kasar ya sanar da kafa gwamnatin kwararru da ba na 'yan siyasa ba.

Sai dai jam'iyar Islama ta Ennahda dake mulki a kasar, ta yi watsi da hakan, tana mai cewa Shugaba Hamadi Jebali "Bai nemi shawarar jam'iyyar ba."

A waje daya kuma 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu bore a birnin Tunis da Gafsa, a cewar rahotanni.

Masu zanga-zanga na Gafsa dake makoki na musamman KaN mutuwar shugaban adawar, sun je ofishin gwamna, inda suka yi ta jifan 'yan sanda da duwatsu da kuma bam da aka hada da fetur.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa lauyoyi da alkalai sun kira yajin aikin kwana biyu saboda kisan Belaid.

Karin bayani