Za a kafa gwamnatin kwararru a Tunisia

Image caption Hamadi Jebali

Firayim Ministan kasar Tunisia, Hamadi Jebali, ya ce zai kafa gwamnatin kwararru bayan da aka hallaka wani shugaban 'yan adawa, Shokri Belaid.

Mista Belaid ya yi kaurin-suna wajen sukar gwamnati kuma kisan sa ya haddasa mummunar zanga-zanga a wadansu biranen kasar, lamarin da hukumomi suka ce ya yi sanadiyar hallaka wani dan sanda.

A jawabin da ya yi ta gidajen talbijin na kasar shugaba Jebali ya ce gwamnatin da zai kafa, wacce ba ta da alaka da 'yan siyasa, za ta tafiyar da al'amurran kasar ne har zuwa lokacin da za a gudanar da zaben kasa baki daya.

Dubban masu zanga-zanga ne suka bukaci gwamnati ta jam'iyar Ennahda da ta sauka daga kan mulki sakamakon kisan da aka yi wa Mista Belaid.

Karin bayani