Shari'ar tsohon Shugaban Chadi

Shugaba Idiss Deby
Image caption Ana tuhumar Hissene Habre, tsohon shugaban Chadi

An bude wata Wata kotu ta musamman a hukumance da aka kafa musamman domin yiwa Tsohon shugaban Chadi mai mulkin kama karya Hissene Habre shari'a a babban birnin Kasar Senegal

Habre dai yana gudun hijira ne a Dakar, tun lokacin da ya rasa ikon Kasar a shekarar 1990, kuma ana zargin sa da aikata laifuka akan bil adama

Kotun ta musamman da aka kafa a wata kasa ta Afirka domin ta yiwa tsohon shugaban shari'a a cikin wata Kasa, ita ce irinta ta farko a Afirka

Fara wannan shara'ar wani muhimman matakine game da gwagwarmaya ta dogon lokaci da wadanda aka ci zarafin su, su ka jima su na yi don ganin tsohon shugaban na Cadi Hissene Habre ya gurfana a gaban kotu.

A na tuhumar shi ne da galazama al'umma ta hanyar gana masu hukuba a lokacin mulkin soji .

Kotun ta mussaman da za ta gudanar da shara'ar an girka ta ne a kasar Senegal , ta na kuma samun goyon bayan kungiyar tarrayar Afrika.

Kamar yadda jagororin gudanar da shara'ar su ka sanar za a gudanar da bincike kafin fara shara'ar gadan -gadan.

Karin bayani