Yajin aikin gama-gari a Tunisia

Masu zanga-zanga a Tunisia
Image caption Masu zanga-zanga a Tunisia na zargin jam'iyyar Ennahda da hannu a kisan jagoran 'yan adawa

Kasar Tunusia na fuskantar yajin aikin gama-gari, da kuma fargabar barkewar karin tashe-tashen hankula yayin da ake jana'izar shugaban ’yan adawa Shokri Bilaid.

An yi fito-na-fito tsakanin ’yan sanda da masu zanga-zanga a Tunis da wadansu wurare jiya Alhamis.

Masu zanga-zangar suna so ne a kawar da gwamnatin kasar wadda jam'iyyar Ennahda ke jagoranta—suna zargin jam’iyyar da hannu a kisan shugaban na ’yan adawa.

Wakilin BBC a Tunis ya ce kasar ta rabu tsakanin masu sassaucin ra'ayi da ke fatan ganin an kafa gwamnatin dimokuradiya irin ta Yamma bayan juyin-juya halin da aka yi a kasar shekaru biyu da suka gabata.

Karin bayani