Janar Allen ya ce NATO ta yi nasara a Afghanistan

Janar John Allen
Image caption Janar John Allen ya shaidawa BBC cewa NATO ta kama hanyar galaba a kan Taliban

Babban Kwamandan dakarun kungiyar tsaro ta NATO da ke Afghanistan mai barin gado, Janar John Allen, ya shaidawa BBC cewa ya yi amanna sun kama hanyar yin galaba a yaki da masu tsattsauran ra'ayin Muslunci na Taliban.

A ranar Lahadi ne dai ake sa ran babban kwamandan zai mika ayyukansa ga wani hafsan sojin na Amurka, Janar Joseph Dunford, yayin wani biki a Kabul.

A wata hirar bankwana da ya yi da BBC, Janar Allen ya yi ikirarin cewa dakarun NATO na samun ci gaba a yakin na Afghanistan.

Sai dai kuma ya yi taka-tsantsan da ya tabo batun ci gaban da aka samu a yunkurin kawo karshen rikicin a siyasance.

Yayin wani taron koli a farkon wannan watan dai, Firayim Minista David Cameron na Birtaniya, da Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan, da kuma Shugaba Asif Ali Zardari na Pakistan sun amince cewa ana bukatar samar da zaman lafiya a Afghanistan cikin gaggawa.

Sun kuma bayyana kudurinsu na assasa wani yunkurin samar da zaman lafiya wanda zai kunshi fara tattaunawa da Taliban a cikin watanni shida.

Sai dai ga alama Janar Allen bai gamsu ba.

A cewarsa, ina ganin wannan wani buri ne mai ban sha'awa, amma kuma mai wahala matuka—bai kamata mu yi shakkar neman zaman lafiya cikin gaggawa ba, amma fa akwai matsala. Zan so in ga an cimma hakan a cikin watanni shida”.

A watanni goma sha taran da Janar Allen ya yi yana jagorancin rundunar ta NATO ya kara mika alhakin tsaron Afghanistan ga sojojin kasar.

Magajin nasa, Janar Dunford, zai sa ido ne a kan janye dakarun kungiyar ta NATO da ke fagen daga wadanda za su koma gida a karshen shekrar 2014.

Karin bayani