Michelle Obama ta halarci jana'izar wata yarinya

Michelle Obama
Image caption Michelle Obama ta halarci jana'izar Hadiya Pendleton

Uwar Gidan Shugaban Kasar Amurka, Michelle Obama, ta halarci jana'izar wata budurwa ’yar Chicago mai shekaru goma sha biyar a duniya wadda aka harbe mako guda bayan ta halarci bikin rantsar da Shugaba Obama.

Daruruwan mutane ne dai suka cika a majami'ar Greater Harvest dake kudancin birnin na Chicago don yin jana'izar budurwar wacce aka ce tana da basira, ga kuma barkwanci da son taimakon jama'a.

Hadiya Pendleton ta taba fitowa a wani faifan bidiyo da ke Allah-wadai da amfani da bindiga don ta da zaune tsaye.

Sai ga shi ita ma harsashin wata bindiga ya yi sanadiyyar mutuwarta a wani wurin shakatawa da ke birnin na Chicago.

Bisa ga dukkan alamu dai wanda ya harbe ta ya zaci ita ’yar wata kungiya ce ta ’yan daba da ba ta ga-maciji da tasa.

Mahaifiyar Hadiya, Cleo Pendleton, ta yi jawabi ga mahalarta jana'izar, wadanda suka hada da ’yan siyasar Chicago da Misis Obama.

A cewarta, “Ba za ku fahimci hakikanin radadin wannan al'amari ba.

“Wadanda suka fahimci wannan radadi a cikinku kuwa, to ina tausaya muku—ba mahaifi ko mahaifiyar da ya kamata a ce sun fuskanci irin wannan al'amari”.

Michelle Obama ba ta ce komai ba saboda iyalan yarinyar sun so su raba jana'izar da siyasa.

Sai dai harbe yarinyar, wanda daya ne daga cikin munanan harbe-harbe arba'in da biyu a Chicago a watan jiya, ya sake jawo hankali ga batun dokokin mallakar bindigogi a Amurka—batun da Shugaban Kasar zai tabo a jawabin da zai yiwa al'ummar kasar a makon da ke tafe.

Karin bayani