Amurka: Dusar ƙanƙara ta shafi sufuri

Yawan dusar ƙanƙara da ta zuba a sassan arewa maso gabashin Amirka ta tilasta rufe hanyoyi da kuma soke zirga zirgar jiragen ƙasa da na sama.

An dakatar da dukkan wasu tafiye tafiye da basu zama wajibi ba yayin da jihohi biyar a yankunan da aka sanya dokar ta ɓaci.

Mutane fiye da dubu dari shidda ne a yanzu haka sune zaune cikin duhu babu wutar lantarki.

An rufe tashar bada wutar lantarki ta Nukiliya dake Massachusetts, hakan nan kuma an kwashe mutanen dake zaune kusa da gaɓar ruwa saboda ambaliyar da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da kuma guguwa mai ƙarfi suka haddasa.