Amurka: Dubban jama'a basu da wutar lantarki

Dubban ɗaruruwan jama'a a arewa maso gabashin Amirka basu da wutar lantarki sakamakon dusar ƙanƙara mai yawa da ke ci gaba da zuba a rana ta biyu a yau.

Tsananin dusar ƙanƙarar ta tilasta rufe tashar wutar lantarki ta Nukiliya dake Massachusetts yayin da wasu jihohi biyar kuma su ma suka dokar ta ɓaci.

An bukaci miliyoyin jama'a mazauna jihohin Massachusetts, da Rhode Island, da Connecticut da New York, da kuma Maine da su kasance a cikin gidajensu.

Wannan matsala ta yanyi dai ta kuma kawo katse hanyoyin sufuri da dama da kuma rufe hanyoyin sadarwa.