Paparoma Benedict ya yi murabus

Paparoma Benedict
Image caption Paparoma Benedict ya ce duniya na sauya wa kuma karfinsa na raguwa

Jagoran mabiya darikar Katolika ta addinin Kirista Paparoma Benedict, zai yi murabus a karshen watan nan a wani abin bazata, kamar yadda fadar Vatican ta tabbatar.

Ya ce ya tsufa da yawa a don haka ba zai iya ci gaba da aikin da aka dora masa ba.

Paparoma Benedict mai shekaru 85 ya zamo Paparoma na 16 a watan Afrilun shekara ta 2005 bayan mutuwar Paparoma John Paul II.

A lokacin da aka zabe shi yana dan shekara 78, shi ne Paparoma mafi tsufa da aka zaba a tarihi.

A wata sanarwa, ya ce: "Bayan na yi tunani kan alakata tsakanina da ubangiji, rashin karfi da kuma tsufa, ban dace da ci gaba da jagorantar wannan darika ba....

Martani

Yanzu haka shugabannin siyasa da addini a duk fadin duniya na ta yabon Paparoma Benedict.

Shugabar gwamnatin Jamus, Angeka Merkel ta kwatanta shi a matsayin shugaban addini mai zurfin tunani na wannan zamani.

Fira Ministan kasar Italiya, Mario Monti, ya ce ya yi matukar girgiza da jin labarin murabus din Paparoma Benedict din.

Fira Ministan Burtaniya, David Cameron ya ce Paparoman ya yi aiki tukuru domin karfafa dangantaka tsakanin Burtaniya da majama'ar mai girma.

Shi kuwa shugaban cocin darikar Anglika, Archbishop Justin Welby cewa ya yi bai ji dadin labarin murabus din Paparoman ba, amma dai ya fahinci dalilin hakan.

Karin bayani