Ghana ta yi zargin fasakaurin zinare zuwa Iran

Shugaban Ghana Dramani Mahama
Image caption Zargin fasakaurin zinare daga Ghana zuwa Iran

Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama, ya baiwa jami'an tsaron kasar sa umarnin gudanar da bincike kan zinaran da kudinsa ya kai miliyoyin daloli da ake zargin anyi fasakaurinsa zuwa kasar Iran.

Mr. Mahama ya ce ya dauki wannan matakin ne bayan da aka zargi Ghana da taimakawa Iran ta kauce takunkumin tattalin arzukin da kasashen yamma su ka kakaba mata.

A watan jiya ne aka kama wani jirgi da ya dauki zinaran da kudinsa ya kai dala miliyan tamanin a birnin Santanbul na kasar Turkiyya

Amma sai dai daga bisani an saki jirgin.

Karin bayani