Sojojin Ghana sama da 120 sun tashi zuwa Mali

Mali
Image caption Sojojin Ghana sun tashi zuwa Mali

An soma jigilar sojojin kasar Ghana sama da dari da ashirin zuwa Mali don su taimaka wajen fatattakar masu kishin Islaman dake kokarin mamaye arewacin Malin.

Sojojin dai sun tashi ne daga filin saukar jiragen saman birnin Accra, a cikin wani katon jirgin saman jigilar sojoji da kayayyakinsu da gwmnatin Burtaniya ta bayar.

Tuni dai Kasashen Najeriya da Nijar su ka tura nasu sojojin domin taimakawa wajen fatattakar 'yan tawaye a arewacin Malin

Ko a ranar litinin, an samu rahotan gwabza fada tsakanin 'yan tawayen da kuma sojoji.

Karin bayani