An kashe akalla mutane 5 a jihar Filato

'Yan sandan Najeriya
Image caption An kashe mutane a Barikin Ladi

Rahotanni daga jahar Plato dake tsakiyar Najeriya na cewa akalla mutane biyar sun rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata, a wani lamari mai nasaba da tashin hankali a karamar hukumar Barikin Ladi dake kusa da birnin Jos.

Lamarin dai ya faru ne yayin da ake ci gaba da samun kisan dauki dai-dai a wasu kauyuka na kewayen Jos babban birnin jihar, a lamura masu nasaba da kabilanci da kuma addini dama na tattalin arziki.

A waje daya kuma rahotanni rundunar 'yan sandan jihar Kano a arewacin Nigeria ta gabatarwa da manema labaru wasu mutane bakwai da tace tana zargin suna da hannu a harin da aka kaiwa mai martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero.

Haka kuma rundunar tace tana neman wasu mutanen da suma ake zargin suna da hannu a harin na Watan janairu, wanda ya janyo mutuwar mutane uku da kuma jikkata wasu da dama.

Karin bayani