'Gwamnatin Yobe na farautar makasan 'yan Korea'

 Taswirar Najeriya
Image caption An yanka likitocin ne a Potiskum sannan aka cire kan daya daga cikinsu

Gwamnatin Jihar Yobe da ke arewa masu gabashin Najeriya ta ce tana farautar wadanda suka aikata kisan gillar da aka yiwa wadansu likitoci ’yan kasar Korea ta Arewa su uku.

Likitocin suna aiki ne a babban asibitin garin Potiskum, birni na biyu mafi girma a Jihar.

An dai yanka likitocin ne sannan aka cire kan daya daga cikinsu.

A wata hira da ya yi da BBC, mai baiwa Gwamnan Jihar shawara a kan harkokin yada labarai, Abdullahi Bego, ya ce gwamnatin ta tsaurara tsaro a duk inda ’yan kasashen waje suke a jihar.

Sai dai kuma ya ce ba zai iya yin magana a madadin ‘’yan sanda ba da aka tambaye dangane da ikirarin da kwamishinan ’yan sandan Jihar ya yi cewa rundunarsa bat a san mutanen na aiki a Potiskum ba balle ta dauki matakan ba su kariya.

Karin bayani