'Yan takara sun yi muhawara a Kenya

Image caption 'Yan takarar shugabancin kasar Kenya

A kasar Kenya, 'yan takarar shugabancin kasa sun gudanar da mahawarar farko wacce aka nuna kai-tsaye ta gidajen talabijin na kasar.

Kodayake 'yan takara takwas ne suka yi mahawarar, amma kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa za a yi fafatawa ta kud-da-kud tsakanin Firayim Minista, Raila Odinga da mataimakinsa, Uhuru Kenyata.

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya na tuhumar Uhuru Kenyatta da hannu a kashe-kashen da aka yi bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekarar 2008.

Ya ce tuhumar da ake yi masa ba za ta hana shi yin takara ba.

Sai dai Raila Odinga ya ce zai yi wuya a gudanar da gwamnatin kasar daga kotun da ke Hague ta hanyar na'urar skype.

'Yan takarar sun bayyana cewa bambance-bambancen kabilanci na yin sanadiyar koma-baya a kasar.

Karin bayani