Korea ta Arewa ta yi gwajin nukiliya

Image caption Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jon-Un

Kasar Korea ta Arewa ta ce ta samu nasarar yin gwajin nukiliya a karkashin kasa karo na uku, abin da kasashen duniya suka yi tur da shi.

Tabbacin ya zo ne sa'oi uku bayan an samu rahotannin wata girgizar kasa ta dan adam a kasar.

Shugaban Amurka, Barrack Obama ya bukaci kasashen duniya su maida martani cikin gaggawa kuma mai zafi ga Korea ta Arewar.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin daukar matakai masu tsauri, idan har Pyongyang ta yi wannan gwajin.

A ranar Talata ne kwamitin tsaro na Majalisar zai tattauna game da batun a New York.

Tun da fari Kafafen watsa labarai na kasar Korea ta kudu sun ce girgizar kasar na da karfin maki biyar da digo daya a ma'aunin ritcher.

Aukuwar girgizar kasar ta nuna cewa watakila an yi amfani da manyan abubuwan da ke fashewa wajen gudanar da gwajin, sabanin gwaje-gwajen da aka gudanar a shekarar 2006 da 2009.

Karin bayani