Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa
Image caption Koriya ta Arewa

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi tir da kakkausar murya da gwajin makamin nukiliyar da Koriya ta Arewa ta yi a yau, wanda shi ne karo na uku.

Ya kuma yi alƙawarin ɗaukar matakan da za su sa Koriyar ta yi watsi da manufarta na kera makamin nukiliyar.

Kwamitin Tsaro ya sha alwashin ɗaukar ƙarin mataki kan batun.

Kafin haka Ƙasar China da Amurka da Koriya ta Kudu duk sun soki lamirin gwajin.

A nata ɓanagren ƙasar Iran na cewa dukkan masu irin wannan suka su lalata nasu makaman nukiliyar kafin su ce kada wasu su mallaka.

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya yi kakkausar suka tare da yin Allah wadai da gwajin makamin nukiliya da Koriya ta Arewa ta yi a karo na uku.

Kwamitin sulhun ya kuma yi alkawarin daukar wasu sabbin matakai domin tilastawa Koriya ta arewa yin watsi da aniyarta ta makamin nukiliya.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Ban Ki-Moon yace mallakar makamin nukiliya barazana ce ga ita kanta Koriya ta arewa amma ba inganta al'amuranta zai yi ba.

Ya ce, “Gwajin nukiliya karo na ukku da Pyongyang ta yi babban kalubale ne ga yunkurin kasashen duniya na daƙile yaɗuwar makaman nukiliya.

Koriya ta Arewa ita ce kadai kasar da ta yi gwajin nukiliya a karni na 21.

Kada mahukuntan Pyongyang su yi tunanin cewa makamin nukiliya zai inganta tsaronsu a maimakon haka zai kara sanya ta cikin ukuba ne da kuma mayar da ita saniyar ware."

Shima Ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu bayyana gwajin ya yi da cewa barazana ce da ba za a lamunta da ita ba kuma ƙalubale ne ga gamayyar ƙasa da kasa.

Ita ma da take tsokaci jakadar Amirka a Majlisar Dinkin Duniya, Susan Rice, ta ce matakin na Koriya ta arewa ya maida da ita baya ga dangi. Insert.

Ta ce "Koriya ta arewa ba ta amfana ba kuma ba za ta amfana ba daga bijire wa dokokin kasa da ƙasa.

Kuma wannan ya ma nesanta ta daga burin da take da shi na na zama kasa mai ƙarfin iko da walwala.

Karin bayani