Ana gudanar da taron gaggawa kan Korea ta Arewa

Image caption Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jon-Un

Kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya na gudanar da wani taron gaggawa bayan da Koriya ta Arewa ta kaddamar da gwajin makamin nukiliya na uku, wanda kuma Kasashen duniya sukai Allawadai da shi

Kwamitin sulhun ya yi barazanar abinda ya kira mahimmin mataki akan Korea ta Arewa, idan har aka kaddamar da wani sabon gwajin makamin nukiliyar.

Kafin taron majalisar dinkin duniyar, Shugaba Obama na Amurka ya bayyana gwajin a matsayin na takala.

Kuma China ta gayyaci jakadan Pyongyang domin ta bayyana masa matukar takaicin ta

Kasar Rasha kuwa ta bukaci Korea ta Arewa data yi watsi da shirin, ta kuma dawo kan teburin tattaunawa

Karin bayani