Paparoma ya yaba wa mabiya Katolika

Paparoma Benedict
Image caption Paparoma Benedict shi ne na farko da yayi murabus a shekaru 600

Dubban masu ibada da suka taru a Fadar Vatican ne, su kayi ta yi wa Paparoma Benedict tafi, a bayyanarsa ta farko a bainar jama'a, tun da aka ba da sanarwar murabus dinsa.

Ya fada wa jama'ar cewa ba shi da karfi a jiki ko na ruhin ci gaba da wannan aiki, kuma zai sauka ne domin ci gaban cocin Roman Katolika.

Paparoman, wanda shi ne na farko da ya yi murabus cikin shekaru 600 nan gaba zai bude addu'ar fara azumin Lent a farfajiyar St Peter.

A karshen wannan watan na Fabreru ne Paparoma zai bar mukaminsa kuma ana saran zabar magajinsa a karshen watan Maris.

'...fa'ida ga chocin...'

Wakilin BBC yace jawabi ne da Paparoman ya saba yi akai-akai a kowacce Laraba to amma wannan ya zo da muhimmanci na musamman.

Paparoman ya kasance cikin nutsuwa da kamala yayin da dubban masu ibada suka rika yi masa tafi kafin ya gabatar da jawabi ga taron jama'ar da suka hallara a fadar Vatican.

Paparoma Benedict cikin kalamai masu taushi da sanyin murya yace zai sauka daga mukamin nasa ne domin amfanin Roman Katolika.

"Na yanke shawarar yin murabus daga wannan matsayi da Allah ya dora ne akai a ranar 19 ga watan Afrilun shekarar 2005. Na kuma yi hakan ne da cikakken 'yanci da fa'ida ga chocin bayan tsawon lokaci ina addu'a da kuma nazari," a cewar Paparoma Benedict.

Ina kuma sane da cewa ba na iya sauke nauyin jagioranci kamar yadda hakan ke bukata da karfin jiki. Abin da ya ci gaba da wanzarwa da kuma haskaka ni shine tabbacin chocin ya dogara ne ga Isa Almasihu wanda kariyarsa da jagoransa ba za su taba gushewa ba. Ina godiya a gare ku duka bisa soyayya da kauna da kuma addu'oin da kuke yi mani."

Karin bayani