An gano kayayyakin hada bom a Gao

Sojan Mali
Image caption 'Yan tawaye na hada bama bamai a Mali

Dakarun Faransa a garin Gao na kasar Mali sun kwace kilo dari biyar na ruwan taki wanda su kai ammana cewa 'yan tawaye na amfani da shi wajan hada bam.

Har ila yau an gano wayoyi da albarusai a wani gida a garin na Gao da aka ce gidan hada bam ne lokacin da dakarun sojin Faransa da na Mali suka sake kwace garin daga hannun 'yan tawayen makwanni 2n da suka wuce.

Wakilin BBC a can ya ce an kara yawan sojojin gwamnati a garin, bayan fadan da aka gwabza ranar lahadi da kuma hare haran kunar bakin waken da aka kai sau biyu a garin.

Yanzu haka jama'a a garin na Gao na zaman dar-dar , yayin da yawancinsu ke zaune a cikin gida bisa rashin sanin tabbas kan abin da ka iya faruwa.

Karin bayani