Kasashen Tarayyar Turai na taro kan sayar da naman doki

Wani wurin sarrafa naman doki
Image caption Wani wurin sarrafa naman doki

Ministoci daga kasashen Turan da ke cikin binciken da ake na naman dokin da aka fitar a matsayin jan nama wato naman shanu da na bisashe, na taro a Brussels domin tattaunawa kan tsauraran dokokin da za a sa kan rubuta suna a jikin kayayyakin abinci.

A makon jiya an gano naman doki a cikin irin naman da ake sawa a tsakiyar biredi wato Burger wanda aka shigar daga Faransa zuwa Birtaniya da Ireland, amma a jiki an rubuta da cewa naman shanu ne.

Masu aiko da rahotanni sun ce sabuwar dokar da ake tattaunawa a kai zata sa a rika bayyana gaskiya game da inda abinci ya fito.

Sai dai masu adawa da dokar na ganin yin hakan zai yi matukar tsada ga kamfanonin dake samar da abinci na duniya.

Karin bayani