Qatar ta baiwa 'yan adawar Syria ofishin jakadancin Syria

'Yan adawar Syria a Qatar
Image caption 'Yan adawar Syria sun sami karbuwa a Qatar

Babbar kungiyar 'yan adawa ta kasar Syria ta ce Qatar ta ba su ofishin jakadancin Syria dake Doha.

Hadakar kungiyar 'yan adawar ta ce tuni ta zabi jakadanta wanda Qatar dauka a matsayin cikakken jami'in dilomasiyya.

Kasashe da dama na daukar hadakar kungiyar 'yan tawayen a matsayin halattaciya dake wakiltar Syria

Qatar ta zama kasa ta farko inda ofishin jakadancin Syria zai kafa tutar 'yan adawar.

Karin bayani