Oscar Pistorius zai fuskanci tuhumar kisa ranar juma'a

Oscar da budurwarsa Reeva
Image caption 'Yan sanda sun ce, sun yi mamakin rahotannin dake cewa Oscar ya harbe Reeva ne, saboda zaton barawo ne

Ana tuhumar zakaran tseren nakasassu na kasar Afrika ta Kudu Oscar Pistorius da kisan budurwarsa a gidansa dake Pretoria.

'Yan sanda sunce an kai mista Pistorius caji ofis, kuma an kashe budurwarsa a gidansa.

Haka kuma sun tabbatar da cewa, za a gurfanar da wani mai shekaru 26 a gaban kuliya a ranar Juma'a.

A kasar Afrika ta Kudu ba a bayyana sunan mutumin da ake tuhuma, har sai an gurfanar da shi a gaban kotu.

Tun da fari dai 'yan sanda sun yi awon gaba da Mr Pistorius a game da lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar budurwarsa.

Yanayin da ya kai ga mutuwarta na da sarkakiya, kodayake ana cigaba da bincike game da kisan.

An harbi Reeva a ka da kuma kirji, kuma ta mutu a gidan Oscar, kafin a kaita asibiti.

Mista Pistorius mai shekaru 26 shi ne mutum na farko da bashi da kafafuwa biyu, da ya fara tsere a gasar Olympics.

Kafafen yada labarai na kasar sun bayyana sunan budurwar da cewa, wata mai tallar kayan kawa ce mai suna Reeva Steenkamp.