An shiga rudanin nadin sabon sakataren tsaron Amurka

Chuck Hagel
Image caption Rudani kan nadin Chuck Hagel a matsayin sakataren Amurka

Batun amincewa da nadin Chuck Hagel a matsayin sabon sakateren tsaron Amurka, ya shiga cikin rudani inda manyan 'yan majalisar dattawa na jam'iyyar Republican suka yi barazanar dakile shi.

Shi dai tsohon Sanata ne a jam'iyyar ta Republican.

Wakiliyar BBC ta ce basu ji dadin kalaman da yayi a baya ba kan Isra'ila da Iran da kuma Iraq, a don haka za su yi amfani da wata dabara da aka dade ana yi amfani da ita a majalisar wurin kawo jinkiri a kada kuri'ar amince wa da shi ko ma a yi watsi da shi kwata-kwata.

'Yan Republican su na neman karin bayani kan abinda shugaban kasa ke yi lokacin da aka kai hari kan ofishin jakadancin Amurka a birnin Benghazi na kasar Libya.

Karin bayani