Mata sun yi zanga-zanga a Lagos

Image caption Taswirar Najeriya

Yau ne wata ƙungiyar mata mai fafatukar kare haƙƙin bil'adama ta gudanar da zanga zangar lumana a Lagos domin nuna rashin amincewa da yunƙurin hukumar babbar birnin tarayya Abuja gina ofishin ƙungiyar matan shugabannin ƙasashen Afurka.

Ƙungiyar na neman shugaban Naijeriya da ya gaggauta umartar ministan babban birnin tarayyar Abuja ya janye shirin gina sakatariyar matan shugabannin Africa da aka ce za ta ci naira biliyon huɗu.

Ƙungiyoyin dai sun ce, bai kmaata gwamnati ta kashe wadannan maƙuden kuɗaɗe wajen gina sakatariyar.

Sai dai kuma hukumar babban birnin tarayya Abuja ta ce, dokar da ta kafa ta bata damar yin ginin.

Abuja dai birni ne dake fama da matsalolin da suka haɗa da na karancin ruwan sha.